Babban taron PDP: Karya ne ban janye ba - Saraki

Babban taron PDP: Karya ne ban janye ba - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Juma’a, 5 ga watan Oktoba yace shi bai janyewa kowa ba kuma ba zai taba janyewa ba a kokarinsa na ganin ya mallaki tikitin takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben fidda gwani da za’a gudanar a karshen mako ba.

Ofishin kamfen din babban dan majalisae ya bayyana cewa rade-radin dake yawo na cewa ya janye duk karya ne da kuma kokarin kawo rudani a tsakanin magoya bayansa.

Babban taron PDP: Karya ne ban janye ba - Saraki

Babban taron PDP: Karya ne ban janye ba - Saraki
Source: Depositphotos

Gabannin babban taron PDP da za’a gudanar a ranar Asabar, 6 ga watan Oktoba, rahotanni sun fara yawo game da cewa wasu yan takara 12 sun janye ma junansu, amma wadanda aka ambata a rahoton sun karyata lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jimi Agbaje ya yi nasarar samun tikitin PDP a Lagas

Da farko mun ji cewa cewa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya hakura da kudirinsa na takarar kujeran shugaban kasa sannan ya marawa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa baya don ganin ya samu tikitin takarar shugabancin kasa na PDP.

A cewar wani shafin yanar gizo, Sahara Reporters, wata majiya na daya daga cikin makusantar ýan takaran ya bayyana cewa Atiku na ta tattaunawa da sauran yan takara irin su Saraki. Majiyar tace:

“Atiku na ta tattaunawa da sauran yan takara irin su Saraki tare da burin ko zasu janye nasu kudirin, don filin ya zama na Atiku da Tambuwal a babban taron jam’iyyar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel