'Yan takarar shugabancin kasa na PDP 5 ne kawai suka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

'Yan takarar shugabancin kasa na PDP 5 ne kawai suka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

- 'Yan takarar shugabancin kasa na PDP biyar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

- Mutane takwas cikin 'yan takarar basu hallarci taron ba kuma ba'a bayyan dalilin da ya hana su zuwa ba

- Ciyaman din PDP, Uche Secondus, ya roki 'yan takarar su kasance tsintsiya madaurinki daya baya zaben

Mutane biyar daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa a PDP sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya gabanin gudanar daa zaben fidda gwani da jam'iyyra za tayi a ranakun 6 da 7 na watan Oktoban Port Harcourt na jihar Rivers.

Wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar na cewa za su cigaba da kasancewa a jam'iyyar duk yadda sakamakon zaben ya kasance sun hada da Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Tsohon gwamna Jigawa, Saminu Turaki, Datti Baba-Ahmed da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.

'Yan takarar shugabancin kasa na PDP sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

'Yan takarar shugabancin kasa na PDP sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
Source: Depositphotos

Ciyaman din jam'iyyar na kasa, Prince Uche Secondus ne ya jagoranci taron a sakatariyar jam'iyyar na Legacy House da ke Maitama, Abuja.

DUBA WANNAN: Buhari ya gwale Oshiomhole: Babu wanda zamu ba tikiti ba tare da zaben cikin gida ba

'Yan takarar da basu hallarci taron ba sun hada da Mataimakin shugban kasa, Atiku Abubakar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanata Ahmed Makarfi, Attahiru Bafarawa, David Mark, Jonah Jang, Stanley Osifo da Gwamna Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe.

A halin yanzu ba'a bayyana takamamen dalilin da yasa sauran 'yan takarar basu hallarci taron ba.

A jawabin da ya yi a taron, Secondus ya tabbatar da cewa jam'iyyar za tayi adalci wajen gudanar da zaben fidda gwanin kuma ya yi kira ga 'yan takarar su hada kansu waje guda bayan zaben fidda gwanin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel