Hukumar INEC ta rarrashi fusatattun shugabanni na jam'iyyar PDP yayin zanga-zangar su

Hukumar INEC ta rarrashi fusatattun shugabanni na jam'iyyar PDP yayin zanga-zangar su

Mun samu rahoton cewa babbar hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta nuna hali irin na dattako wajen tunkarar fusatattun shugabanni na jam'iyyar adawa ta da suka gudanar da zanga-zanga a gaban ofishinta dake birnin tarayya na Abuja.

Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun aiwatar da zanga-zangar su ta lumana domin bayyana takaicin su kan dambarwar zaben gwamnan jihar Osun da ya wakana makon da ya gabata.

A sanadiyar haka cikin nuna hali na dattako hukumar INEC ta tari numfashin kusoshin jam'iyyar ta PDP tare da rarrashin su da kalamai da lafuzza masu dadi domin kwantar ma su da hankali.

Hukumar da sanadin kwamishinonin ta biyu, May Agbamuche-Mbu da kuma Muhammad Haruna, sun rarrashin fusatuwar jiga-jigan jam'iyyar ta hanyar bayar da amincinsu kan tabbatar da gaskiya da adalci yayin gudanar da babban zabe na 2019.

Hukumar INEC ta rarrashi fusatattun shugabanni na jam'iyyar PDP yayin zanga-zangar su

Hukumar INEC ta rarrashi fusatattun shugabanni na jam'iyyar PDP yayin zanga-zangar su
Source: Twitter

Jiga-jigan jam'iyyar da suka halarci wannan zanga-zanga sun hadar da; shugaban jam'iyyar na kasa, Prince Uche Secondus, shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal da kuma Sanata Kano ta tsakiya, Rabi'u Kwankwaso.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari, Oshiomhole, Oyetola da Aregbesola sun shiga bayan Labule a Fadar Villa

Sauran kusoshin jam'iyyar sun hadar da Sanata Dino Melayet na jihar Kwara, Sanata Ben Bruce na jihar Bayelsa, tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da kuma shugaban jami'ar Baza, Datti Baba Ahmed.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin aiwatar da wannan zanga-zanga cikin lumana, hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta kuma tirnike kusoshin jam'iyyar da Barkonon Tsohuwa.

Nan ba da jimawa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu a gare ku yayin kasancewar ku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel