Dalilin da ya sa ban goyi bayan Adeleke a zaben Osun zagaye na 2 ba - Omisore

Dalilin da ya sa ban goyi bayan Adeleke a zaben Osun zagaye na 2 ba - Omisore

- Sanata Iyiola Omisore ya bayyana dalilinsa na goyon bayan APC tare da juyawa Adeleke baya a zaben jihar Osun zagaye na biyu

- Ya ce shuwagabannin jam'iyyar PDP na jihar ne suka ce ba sa bukatar goyon bayansu ta hanyar hana Atiku Abukar ganawa da shi

- Mun kulla yarjejeniya da APC tare da fatan cewa Osun zata zamo kamar sauran jihohi koma ta zarce su

Dan takarar gwamnan jihar Osun a zaben da ya gudana na jihar karkashin jam'iyyar SDP, Sanata Iyiola Omisore, ya ce ya zabi goyon bayan dan takarar jam'iyyar APC, Alhaji Gboyega Oyetola, a zaben gwamnan jihar zagaye na biyu saboda shuwagabannin jam'iyyar PDP na jihar ne suka ce ba sa bukatar goyon bayansu.

Omisore ya bayyana hakan a garin Osogbo a ranar Alhamis a wani taro da mambobin jam'iyyar SDP da suka fito daga kananan hukumo 30 na jihar.

Omisore, wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa SDP watannin baya gabanin zaben gwamnan jihar, ya ce tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar, ya shirya zuwa don tattaunawa da shi kafin gudanar da zaben zagaye na biyu a lokacin da ya ziyarci Osogbo, amm sai shuwagabannin jam'iyyar PDP suka hana Atiku yin hakan.

KARANTA WANNAN: Cikin wata 1: Hukumar kwastam ta cafke motoci 22 da kudinsu ya kai N2bn

Dalilin da ya sa ban goyi bayan Adeleke a zaben Osun zagaye na biyu ba - Omisore

Dalilin da ya sa ban goyi bayan Adeleke a zaben Osun zagaye na biyu ba - Omisore
Source: Depositphotos

Wani tsohon jakadan Nigeria a kasar Philippines, Dr. Yemi Farounbi, ya taba bayyana hakan a lokacin da yake fayyace dalilan da suka sanya Omisore goyon bayan dan takarar APC a zagaye na biyu na zaben gwamnan jihar da ya gudana a ranar 27 ga watan Satumba.

Omisore ya ce: "Ina so in dora akan dukkanin jawaban da Dr. Farounbi ya gabatar. Mun baiwa jam'iyyar APC da PDP bukatunmu. Mun bukace su akan duk wanda ya ci zabe zai biya basussukan da ma'aikata ke bi na albashi, fansho da giratuti, da kuma daukar matasanmu aiki tare da sake fasalin ilimi na jihar da dai sauransu.

"Mun shiga yarjejeniyar ne da kyakkyawar zuciya da fatan cewa Osun zata zamo kamar sauran jihohi koma ta zarce su. Sai ga shi dai Allah ya sanya hakan za ta kasance karkashin mulkin APC idan har sun cika alkawuran da suka daukar mana" a cewar Omisore.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel