Karya ne, babu yadda za’ayi in janyewa Tambuwal – Dankwambo ya karyata rahoto janye takararsa

Karya ne, babu yadda za’ayi in janyewa Tambuwal – Dankwambo ya karyata rahoto janye takararsa

Yayinda ake shirye-shiryen zaben fidda gwanin kujerar shugaban kaka karkashin jam’iyyar PDP gobe, Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karyata rahoton cewa shi da wasu yan takara zasu janyewa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tabuwal.

Dankwambo ya mayar da martani ga jaridar Sahara Reporters kan labarin da suka wallafa cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark; tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido; da shi sun amince da janyewa gwamna Aminu Waziri Tambuwal a zabn fidda gwanin da zai gudana gobe Asabar, 6 ga watan Oktoba, 2018.

Dankwambo yace:

“Karya ne”

“Ni gwamna mai zamani biyu ne”

“Na kasance mai biyayya ga jam’iyyar PDP”

“Wannan abu ya sabawa hankali”

“Wannan bogi suka baku”

KU KARANTA: Shahrarren dan majalisan nan Gudaji Kazaure ya samu nasara a zaben fidda gwani

Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP tana shirin taron gangaminta da zaben fidda gwanin shugaban kasa gobe a birnin Fatakwal, jihar Ribas.

Yan takara 12 ne zasu kara da juna a zaben gobe, ga jerin sunayensu:

1. Atiku Abubakar

2. Abubakar Saraki

3. Rabiu Kwankwaso

4. Ibrahim Dankwambo

5. David Mark

6. Tanimu Turaki

7. Aminu Tambuwal

8. Jonah Jang

9. Datti Baba Ahmed

10 Dr. Sule Lamido

11. Ahmad Makarfi

12.Attahiru Bafarawa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu. Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel