Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya janye ma Atiku

Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya janye ma Atiku

Rahotanni dake billowa sun yi ikirarin cewa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya hakura da kudirinsa na takarar kujeran shugaban kasa sannan ya marawa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa baya don ganin ya samu tikitin takarar shugabancin kasa na PDP.

A cewar wani shafin yanar gizo, Sahara Reporters, wata majiya na daya daga cikin makusantar ýan takaran ya bayyana cewa Atiku na ta tattaunawa da sauran yan takara irin su Saraki.

Majiyar tace: “Atiku na ta tattaunawa da sauran yan takara irin su Saraki tare da burin ko zasu janye nasu kudirin, don filin ya zama na Atiku da Tambuwal a babban taron jam’iyyar.

Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya janye ma Atiku

Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya janye ma Atiku
Source: Depositphotos

“Bana tunanin zai amince amma abun da nasani shine yana fuskantar matsin lamba,” inji ajiya na biyu wanda ya nemi a boye sunansa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da Anyim

“An matsa masa; ana ta tattaunawa, sannan ana ta Magana kan ya hakura ya janye ma Atku. Mataimakin shugaban kasar na kokari gina hadin gwiwa; idan Saraki ya janye masa, hakan na nufin zai samu dama saboda wakilan Sarak zasu koma bayansa.

“Ban san abunda Saraki zai yanke ba, amma zan iya tabbatar a cewa eh yana fuskantar matsin lamba don ya janye ma Atiku.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel