Zanga-zangan zaben Osun: Shugabannin PDP na da matsala a kwakwalwa – Aregbesola

Zanga-zangan zaben Osun: Shugabannin PDP na da matsala a kwakwalwa – Aregbesola

Gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a ranar Juma’a, 5 ga watan Oktoba ya bayyana shugabannin babban jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da suka yi zanga zanga a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta kan sakamakon zaben gwamnan jihar a matsayin “masu tabin hankali”.

Aregbesola ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya gabatar da zababben gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Zanga-zangan zaben Osun: Shugabannin PDP na da matsala a kwakwalwa – Aregbesola

Zanga-zangan zaben Osun: Shugabannin PDP na da matsala a kwakwalwa – Aregbesola
Source: Depositphotos

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus na daga cikin shugabannin da suka yi zanga-zanga akan sakamakon zben a hedkwatar INEC dake Abuja.

KU KARANTA KUMA: Zaben cikin gida: 'Yan takara sunyi zanga-zangar rashin amincewa da zabe a Kano

A halin da ake ciki, mun ji cewa jami'an yan sandan Najeriya sun watsawa shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP barkonon tsohuwa yayinda suke gudanar da zanga-zanga zuwa ofishin hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC a yau.

Mun kawo muku rahoton cewa Shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na gudanar da zanga-zanga kan sakamakon zaben jihar Osun da aka kammala kwanan nan na gwamna.

Masu zanga-zangan na neman INEC ta kaddamar da dan takarar PDP Ademola Adeleke a matsayin wanda yayi nasara a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel