Hukumar EFCC ta tasa keyar Sanata gaban kotu kan zargin wawure naira miliyan 322

Hukumar EFCC ta tasa keyar Sanata gaban kotu kan zargin wawure naira miliyan 322

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta sake tasa keyar wani Sanatan Najeriya a karo na biyu bisa zarginsa da satar kudi naira miliyan dari uku da ashirin da biyu (N322m), inji rahoton Sahara reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito EFCC ta shigar da dan majalisa mai wakiltar Delta ta Arewa, Sanata Peter Nwaboashi ne gaban babbar kotun tarayya dake garin Legas a karkashin jagorancin mai sharia C.J Aneke.

KU KARANTA: Wani Gwamna a Najeriya ya garkame gidan tsohon gwamnan jaharsa

Hukumar tana zargin Sanata Peter ne da wasu kamfanoni guda biyu da suka hada da kamfanin Golden Touch construction project ltd, da Suiming Electricals Ltd, wadanda take zarginsu da hannu cikin badakalar sayen gida na naira miliyan 805.

Hukumar EFCC ta tasa keyar Sanata gaban kotu kan zargin wawure naira miliyan 322

Nwaboashi
Source: Facebook

Da fari, sai da EFCC ta bayyana ma kotu dalla dalla tuhume tuhumen da take dasu akan Sanatan da kamfanonin guda biyu, inda tace Sanatan da kamfanin Golden touch sun saye wani gida dake titin Marine a unguwar Apapa ta jahar Legas akan kudi naira miliyan dari takwas da biya a shekarar 2014.

Sai dai EFCC ta yi zargin cewa miliyan dari uku da ashirin da biyu daga cikin wannan kudi haramtattu ne, inda tace an samesu ne ta hanyar damfara, kuma kamfanin Suiming ce ta biya dillalin gidan wadannan kudade.

EFCC ta cigaba da fadin cewa kamfanin Suiming ce ta taimaka ma Sanatan da kamfanin Golden Touch wajen sayan wannan gida da kudaden damfara, wanda tace hakan ya saba ma sashi na 18 (a), 15 (2) (d) na kudnin dokokin hana sata, haka zalika hukuncinsa na kunshe cikin sashi 15 (3).

Sai dai dukkanin wadanda ake tuhuma sun musanta tuhume tuhumen da EFCC ke yi musu, inda lauyansu ya bukaci kotu da ta kyalesu su cigaba da cin moriyar belin da suka samu tun a kotun baya, sa’nnan ya bukaci Alkalin ya baiwa Sanatan fasfonsa na fita kasashen waje don ya samu damar tafiya kasar Indonesia.

Daga karshe Alkali Aneke ya bada umarnin a baiwa Sanatan fasfonsa, sa’annan ya umarce shi daya tabbata ya dawo da fasfon ga Kotu zuwa ranar 23 ga watan Oktoba, sa’annan y adage zaman sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel