Yanzu-yanzu: Yan sanda sun watsa wa Bukola Saraki, Sule Lamido, Tambuwal barkonon tsohuwa

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun watsa wa Bukola Saraki, Sule Lamido, Tambuwal barkonon tsohuwa

Jami'an yan sandan Najeriya sun watsawa shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP barkonon tsohuwa yayinda suke gudanar da zanga-zanga zuwa ofishin hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC a yau.

Daga cikin shugabannin jam'iyyar da suka tafi zanga-zangar sune shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; gwamnan jihar Sokoto, AMinu Waziri Tambuwal; shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus; dan takaran kujeran shugaban kasa, Sule Lamido da shugaban jami'ar Baze University, Datti Baba Ahmed.

Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbodiyan, ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Tuwita a yau Juma'a, 5 ga watan Oktoba, 2018.

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun watsa wa Bukola Saraki, Sule Lamido, Tambuwal barkonon tsohuwa

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun watsa wa Bukola Saraki, Sule Lamido, Tambuwal barkonon tsohuwa
Source: Twitter

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun watsa wa Bukola Saraki, Sule Lamido, Tambuwal barkonon tsohuwa

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun watsa wa Bukola Saraki, Sule Lamido, Tambuwal barkonon tsohuwa
Source: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa Shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na gudanar da zanga-zanga kan sakamakon zaben jihar Osun da aka kammala kwanan nan na gwamna.

Masu zanga-zangan na neman INEC ta kaddamar da dan takarar PDP Ademola Adeleke a matsayin wanda yayi nasara a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel