Tambuwal ne ke da karfin da zai iya kayar da Buhari a 2019 - Kungiya

Tambuwal ne ke da karfin da zai iya kayar da Buhari a 2019 - Kungiya

Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa a PDP, Aminu Waziri Tambuwal na da abun da ake bukata waajen kayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019 inji kungiyar magoya bayansa.

A cewar kungiyar hakan zata kasance idan har za’a gudanar da zabe na gaskiya da amana.

Kungiyar magoya bayan Tambuwal sunyi Magana ne a wata wasika da suka aike ga wakilan da zasu gudanar da zaben fidda dan takarar shugaban kasa a PDP a gobe.

Tambuwal ne ked a karfin da zai iya kayar da Buhari a 2019: Kungiya

Tambuwal ne ked a karfin da zai iya kayar da Buhari a 2019: Kungiya
Source: Depositphotos

Suna rokon ýayan jam’iyyar da su mallakawa Tambuwal tikitin takara a PDP.

KU KARANTA KUMA: Bakwai ga Oktoba zamu rufe karbar sunayen 'yan takarkaru daga jam'iyyu - INEC

A cewarsu gwamnan Sokoton bai da guntun kashi makale da shi da gwamnatn Buhari zata yi amfani da shi wajen yin nasara a kan sa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na gudanar da zanga-zanga zkan sakamakon zaben jihar Osun da aka kammala kwanan nan na gwamna.

Shugabannin na PDP sun hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara da shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus ne suke jagorantar zanga-zangar zuwa hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a Abuja.

Masu zanga-zangan na neman INEC ta kaddamar da dan takarar PDP Ademola Adeleke a matsayin wanda yayi nasara a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel