Akwai yiwuwar Najeriya za ta fuskanci karancin Shinkafa a 2019 - Audu Ogbeh

Akwai yiwuwar Najeriya za ta fuskanci karancin Shinkafa a 2019 - Audu Ogbeh

Mun samu rahoton cewa gwamnatin tarayya ta yi gargadi gami da jan jan kunne na hararo yiwuwar aukuwar annoba ta karancin Shinkafa cikin kasar nan ta Najeriya a shekara mai gabatowa muddin ba a dauki kwararan mataikai ba.

Ministan harkokin noma da raya karkara, Mista Audu Ogbeh, shine ya yi wannan gargadi kamar yadda shafin jaridar Today Nigeria ya ruwaito.

Mista Ogbeh ya bayyana cewa, muddin ba bu wata shimfida ta kwararan matakai da za su tabbatar da riga kafi kan aukuwar annobar ambaliyar ruwa to kuwa ba bu shakka za a fuskanci matsanancin karanci na shinkafa cikin kasar nan a badi.

Ministan ya bayyana hakan ne cikin jawabansa yayin halartar wani taro kan harkokin noma da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya a jiya Alhamis.

Akwai yiwuwar Najeriya za ta fuskanci karancin Shinkafa a 2019 - Audu Ogbeh

Akwai yiwuwar Najeriya za ta fuskanci karancin Shinkafa a 2019 - Audu Ogbeh
Source: Depositphotos

Yake cewa, aukuwar ambaliyar ruwa ta illata wasu jihohin kasar na dake sama ta fuskar samar da kuma noman shinkafa musamman jihohin Kebbi, Jigawa, Anambra da kuma Kogi, inda manoma da dama suka yi koken asarar amfani na gonakin su.

KARANTA KUMA: Zaben Fidda Gwani: Wakilan Jam'iyyar PDP sun raba Gari tsakanin Tambuwal da Bafarawa

Kazalika Ministan ya yi kira tare da neman tsayuwar daka wajen dakile wannan mummunar annoba da ta fuskanto kasar nan a halin yanzu da cewar muddin ba haka ta na iya shafar kayan abinci na hatsi irin su Gero, Gawa da kuma Masara.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Ima Nibori, wani hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, zai nemi takarar kujera ta Majalisar Wakilai a karkashin jam'iyyar APC.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel