Hukumar FIRS mai tara haraji ta kasa, ta kwato kusan biliyan hudu daga wata cuwa-cuwa da ta kama

Hukumar FIRS mai tara haraji ta kasa, ta kwato kusan biliyan hudu daga wata cuwa-cuwa da ta kama

A rahoton ta da ta fitar, hukumar karba da tara haraji ta kasa, tace a tsakanin watan daya na 2017, zuwa watan Agusta na 2018, ta kwato N3.63b daga kamfanoni da jama'a masu gujewa biyan haraji, da masu itar da kudi ba bisa ka'ida ba, da ma masu boye kasuwancin.

Hukumar FIRS mai tara haraji ta kasa, ta kwato kusan biliyan hudu daga wata cuwa-cuwa da ta kama

Hukumar FIRS mai tara haraji ta kasa, ta kwato kusan biliyan hudu daga wata cuwa-cuwa da ta kama
Source: Instagram

A rahoton ta da ta fitar, hukumar karba da tara haraji ta kasa, tace a tsakanin watan daya na 2017, zuwa watan Agusta na 2018, ta kwato N3.63b daga kamfanoni da jama'a masu gujewa biyan haraji, da masu itar da kudi ba bisa ka'ida ba, da ma masu boye kasuwancin.

Shugaban hukumar ne ke fadin haka a jiya a Abuja, yayi taronsu da hukumomin kasashen Afirka AU wadanda suma ke kula da irin wannan ayyuka a kasashensu.

Mista Tunnde Fowler, yace wasu kudaden kuma basuka ne na haraji da ake bin wasu da suka ki biya.

DUBA WANNAN: Anyi kira ga Buhari ya kori wasu alkalai biyu masu cin hanci

Irin wadannan halayya dai, ita ta hana kasashen Afirka ci gaba, da ma baragurbin shugabanni, masu kwashe kudi da kasuwancin su zuwa kasashen waje su boye.

An mai da filaye ma hannun gwamnati, daga kamfanunuwa 114 da suka amshe su a mulkin baya, ba bisa ka'ida ba, a wadanda kamfunnan wasu ma sunce basu san an basu wadannan filaye ko da sunansu ba, yace kotu ce zata bi kadin sauran bayanai, ta hannun ofishin antoni janarr na kasa.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel