Bakwai ga Oktoba zamu rufe karbar sunayen 'yan takarkaru daga jam'iyyu - INEC

Bakwai ga Oktoba zamu rufe karbar sunayen 'yan takarkaru daga jam'iyyu - INEC

- Ana tsaka da zabukan cikin gida na jam'iyyu

- INEC tace baza ta qara koda kwana daya ba, zata rufe karbar sunaye

- Su dai jam'iyyu na kira a kara musu lokaci

Bakwai ga Oktoba zamu rufe karbar sunayen 'yan takarkaru daga jam'iyyu - INEC

Bakwai ga Oktoba zamu rufe karbar sunayen 'yan takarkaru daga jam'iyyu - INEC
Source: Depositphotos

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, tace babu qarin koda kwana daya don jam'iyyu su ci gaba da zabukan cikin gidansu daga bakwai ga wannan wata, inda wasu jam'iyyun ke ganin sai an dage musu kafa don su kammala warware rigingimun da ke bulla a cikin jam'iyyun.

A cewar kakakin hukumar, mai kula da fitar bayanai daga hukumar, yace cikin jam'iyyu 91, 89 tuni dama sun fara zabukansu na cikin gida.

A wasu jam'iyun dai, rigima ta hana a san waye dan/yar takarar kujerunsu, bayan yagewar jam'iyyun biyu, inda kowanne bangare ke tutiyar shine da iko.

DUBA WANNAN: Lantarki daga hasken rana mafi girma a Kano

A litinin ne ake sa rai za'a ga waye dan takarar jam'iyyar PDP mai dawa, wanda ana sa rai shine zai kara da na APC a zabukan, jam'iyyu biyu da suka fi kowanne karfi a kasar nan.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel