Kashe-kashe: Ya kamata a tsige Shugaba Buhari don dole – HURIWA

Kashe-kashe: Ya kamata a tsige Shugaba Buhari don dole – HURIWA

Mun samu labari daga Jaridar The Concise News cewa Kungiyar HURIWA ta Marubutan Kasar nan ta nemi a fara shirin tunbuke Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Majalisar Tarayyar Najeriya.

Kashe-kashe: Ya kamata a tsige Shugaba Buhari don dole – HURIWA

Kungiyar HURIWA na nema a tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Source: Depositphotos

Wannan kungiya ta HURIWA mai zaman kan-ta ta fara wannan kira ne a dalilin kashe-kashen da ake yi a kasar wanda ya ki karewa har yau. Kungiyar tace Gwamnatin Buhari ta gaza kawo karshen wannan bala’i don haka ya kamata a tsige ta.

Shugaban wannan Kungiyar a Najeriya Mista Emmanuel Onwubiko da kuma babban Darektan ta na yada labarai watau Zainab Yusuf ne su ka sa hannu a wani jawabi da aka fitar jiya Alhamis inda su ka nemi ayi waje da Shugaba Buhari.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar Kano ya sha kashi a hannun wani Mai ba Osinbajo shawara

HURIWA ta na magana ne kan abin da yake faruwa a Jihar Filato da kuma sauran bangarorin Arewa maso tsakiyar Najeriya inda aka kashe dubban mutanen Kasar. Daga ciki akwai harin da aka kai har cikin Jami’ar da ke Garin Jos.

Kungiyar mai zaman kan-ta, ta kuma soki Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong wanda ake wannan kashe-kashe a Jihar sa a gaban sa. A jawabin, Kungiyar ta koka da yadda Makiyaya ke tada hatsaniya ba tare da an dauki wani mataki ba.

Jiya jun ji cewa Shugaban Hafsun Sojin Najeriya Tukur Buratai ya bayyana cewa shakka babu akwai sa-hannun wasu manya a rikicin da ke aukuwa a Jihar Filato wanda ya ki ci ya ki cinyewa har ila yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel