Gwamnatin Najeriya ta dauki sabon alkawari game da matatun man Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta dauki sabon alkawari game da matatun man Najeriya

Karamin ministan mai kuma tsohon shugaban hukumar tace man fetir ta kasa, Mista Ibe Kachikwu ya bayyana cewa kafatanin matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya zasu fara aiki ganga ganga zuwa karshen shekarar 2019.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mista Ibe ya bada tabbacin ne a yayin taron kaddamar da ginin karamar matatar mai mai tace gangan danyen mai dubu biyar a kowane rana a karamar hukumar Ohaji/Egbema na jahar Imo a ranar Alhamis 4.

KU KARANTA: Yan APC a majalisa sun bayyana matakin da zasu dauka akan Dogara da zarar ya bude majalisa

Hukumar sa ido akan baiwa yan kasa aiki da sa ido a harkar man fetir, NCDMB ne da kamfanin tace man fetir na Walter Smith Petro-Chemical Limited zasu hada karfi da karfe wajen gina wannan matatar man.

A jawabinsa, Ibe yace gwamnatin Buhari ta dage tukuru wajen ganin matatun man Najeriya sun fara aiki a shekarar 2019; “Ba abun farin ciki bane idan har bamu daina siyo man fetir daga kasashen waje ba kafin karshen shekarar 2019.

“Don haka muka jajirce wajen gyaran matatun man, idan har aikin ya kammala, zamu ya tace gangan danyen mai dubu dari biyar a ranar, manufarmu itace tace akalla kasha ashirin na man fetir da muke amfani da shi, sa’annan mu kai ga kashi hamsin zuwa shekaru biyar masu zuwa.” Inji shi.

A jawabinsa, babban sakataren hukumar NCDMB, Kasiye Wabote yace hukumar za ta zuba hannun jarin dala miliyan goma ne a wannan aikin gina matatan man, kamfanin da yace yana sa ran zai fara aiki a nan da watanni goma sha takwas.

Dayake nasa jawabin, shugaban kamfanin Walter Smith, Malam Abdulrazak Isa yace a shekarar 2011 suka fara kirkirar gina matatar man don rage yadda ake shigo da tataccen mai daga kasashen waje a Najeriya.

“Idan kamfanin ta fara aiki, zamu dinga samar da lita dubu hamdin da hudu sittin da casa’in da daya na kalanzir, sai kuma lita dari uku da dari da sittin da takwas na iskar gas.” Inji Malam Isa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel