Gwamna Fayose yana neman fansar Biliyoyi wajen Hukumar EFCC

Gwamna Fayose yana neman fansar Biliyoyi wajen Hukumar EFCC

Mun samu labari cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Ekiti wanda ke shirin barin karagar mulki watau Ayodele Peter Fayose yana neman Hukumar EFCC ta biya sa kudi a dalilin ci masa zarafi da tayi.

Gwamna Fayose yana neman fansar Biliyoyi wajen Hukumar EFCC

Fayose yana neman EFCC ta biya sa wasu makudan Biliyoyin kudi
Source: Depositphotos

Gwamna Fayose yayi kira ga Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta ba shi Naira Biliyan 20 sannan kuma ta ba shi hakuri a gaban Duniya na wulakanta sa da tayi a bainar Jama’a kwanaki.

Kwanaki Hukumar EFCC ta fitar da sunan Gwamman cikin wadanda ta ke dako don haka Fayose wanda yake daf da kammala wa’adin sa ya so a nemi afuwar sa a manyan gidan Jaridu akalla 3 na kasar nan a matsayin sa na Gwamna.

KU KARANTA: An bankado yadda ake tursasa matan Najeriya karuwanci

Gwamna Ayodele Fayose ya bayyana wannan ne ta bakin mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai watau Olayinka Lere. Gwamnan yace idan EFCC ba ta cika sharudan sa ba zai shiga Kotu da ita nan da kwana 3 masu zuwa.

Tuni dai har Gwamnan ya fara shirin shigar da kara a gaban Kotu ta bakin wani babban Lauyan sa Obafemi Adewale. Yanzu dai takaradar Gwamnan na PDP ta shiga hannun Hukumar ta EFCC a Hedikwatar ta da ke Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel