PDP na zargin APC da yunkurin dakatar da ita daga gudanar da babban taronta na kasa

PDP na zargin APC da yunkurin dakatar da ita daga gudanar da babban taronta na kasa

- Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewar APC na shirya makircin hanata gudanar da babban taronta da zata gudanar a garin Fatakwal

- PDP ta ce APC na tsoron wannan taro nata wanda zata fitar da dan takarar shugaban kasar da zai kara da Buhari a zaben 2019

- Sai dai jam'iyyar ta bugi kirji da cewar babu wata barazana da zata dakatar da ita daga gudanar da taron kamar yadda ta tsara

Jam'iyyar PDP ta ta yi ikirarin cewa tana zargin jam'iyya mai mulki ta APC na kammala shorye shiryen tayar da zaune tsaye da haddasa rikici a yayin da jam'iyyar ta PDP zata gudanar da babban zabenta na kasa a ranar Asabar da Lahadi, a garin Fatakwal don gudanar da zaben fid-da gwani.

Sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar PDP, Kola Ologbinduyan ya yi wannan zargin a wani taron ganawa da manema labarai a babban sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja a ranar Alhamis, 04 ga watan Oktoba.

"Ana wani yunkuri da jam'iyya mai mulki ta ke yi na kawo hatsaniya a babban zaben da muka shirya gudanarwa. Muna sane da take taken APC na tsoron da ta ke yi mu gudanar da taron, don sun san zamu fitar da dan takara da zai kara da Buhari kuma ya yi nasara akansa a zaben 2019," a zargin Ologbondiyan.

KARANTA WANNAN: Kungiyar Musulman jihar Oyo sun bukaci Ajimobi a samar da kotun shari'ar musulunci

PDP na zargin APC da yunkurin dakatar da ita daga gudanar da babban taronta na kasa

PDP na zargin APC da yunkurin dakatar da ita daga gudanar da babban taronta na kasa
Source: UGC

Ko da aka tambaye shi cikakken shirin APC na haddasa fitina a taron nasi, mai magana da yawun PDP ya ce "zata iya aikata hakan ta kowacce siga; ko ta zuwa kptu, ko dai ta fuskar da ta so, don haka muke sanar da 'yan Nigeria da su san halin da ake ciki na kokarin hanamu gudanar da babban taro"

Sai dai ya bugi kirji da bada tabbacin cewa babu wata barazana ko tada zaune tsaye da zai hana jam'iyyar PDP gudanar da zaben fitar da dan takarar shugaban kasarta kamar yadda ta tsara gudanarwa.

Ya ce jam'iyyar ta aikawa duk wata hukuma ta gwamnati takardar sanarwa na yunkurin PDP npna gudanar da babban taron a Fatakwal. Ya kuma ce a garin Fatakwal dinne za a tantance masu kowa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel