Mun tura Kwankwaso PDP ne domin ya yi mana wani aiki - Jigo a APC

Mun tura Kwankwaso PDP ne domin ya yi mana wani aiki - Jigo a APC

A yayin da PDP a jihar Kano ke cigaba da fama da rigingimu tsakanin tsagin Kwankwasiyya da ragowar 'yan jam'iyyar, wani jigo a jam'iyyar APC ya ce da ma sun san hakan zata faru.

Da yake magana da wakilin gidan talabijin din Liberty a ofishinsa, jigo a APC kuma kwamishinan kasa da raya karkara a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewar babu abinda zai hana Sanata Kwankwaso daga karasa rusa jam'iyyar PDP a Kano.

"Ai yanzu a Kano babu jam'iyyar PDP sai dai Kwankwasiyya. Ya shigo ya samu jam'iyya amma saboda zalunci ya kwace ragamar gudanar da tafiyar da al'amura ta karfin tsiya.

"Yanzu ya fito da yaronsa ya ce shine dan takarar gwamna a PDP, su kuma ragowar 'yan takara sun ce basu yarda ba su ma sai sun gudanar da nasu zaben domin fitar da dan takarar gwamna na gaskiya.

Mun tura Kwankwaso PDP ne domin ya yi mana wani aiki - Jigo a APC

Kwankwaso
Source: Twitter

"Sun garzaya sun tafi Abuja neman uwar jam'iyyar PDP ta shiga maganar, amma ni shawarar da zan ba su shine su daina bata lokacinsu su dawo mu hada kai domin dafa wa gwamna Ganduje da shugaba Buhari.

"Mu ne mu ka tura Kwankwaso PDP ta karkashin kasa domin ya karasa aikin da ya dauki alkawari na rusa PDP.

DUBA WANNAN: Ya mare shi, shi kuma ya cije shi: Hadiman Buhari biyu sun yi fada a kan zaben fitar da dan takarar gwamna a APC

"Shi da bakinsa ya fada cewar sai ya rusa PDP kuma yanzu kowa na ganin yadda yake karasa rugurguza jam'iyyar," a cewar Musa Iliyasu.

Kwankwaso na cigaba da fuskantar tirjiya daga wurin 'yan jam'iyyar PDP a jihar Kano, musamman wadanda suka sayi fam din takarar kujeru daban-daban karkashin PDP din a Kano.

Kwankwaso ya tsayar da surukinsa, Abba Kabir Yusif, a matsayin dan takarar gwamnan Kano a PDP, lamarin da ragowar 'yan takarar suka ce sam basu yarda da shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel