Hukumar Kotuna ta kasa ta sauke alkalai biyu bisa zargin cin hanci da rashawa

Hukumar Kotuna ta kasa ta sauke alkalai biyu bisa zargin cin hanci da rashawa

- A baya an taba kaiwa alkalai samame kan sata ca cin hanci

- An dawo da wasunsu, an kuma yiwa wasunsu ritya

- Yanzu an binciki wasunsu an kuma sallame su

Hukumar Kotuna ta kasa ta sauke alkalai biyu bisa zargin cin hanci da rashawa

Hukumar Kotuna ta kasa ta sauke alkalai biyu bisa zargin cin hanci da rashawa
Source: Depositphotos

Hukumar EFCC, tare da hukumar NJC, watau hukumar shari'a, sun mika sunayen manyan alkalai biyu na kasar nan da suke so shugan ya kora, bayn bincike ya same su dumu-dumu da laiffin karbar rashawa da cin hanci.

Alkalan dai sun hada da Jastis Rita Ofili-Ajumogobia ta Federal High Court watau kotun tarayya, sai kuma Jastis James Agbadu-Fishim na kotun masana'antu, watau national industrial court of Nigeria.

DUBA WANNAN: Yadda Osama bin Laden ya aiko wa Boklo HAram kudaden jihadi

Alkalan, baya da aka kai koken yadda suke tafikar da aayyukansu, kuma bincike ya nuna lallai akwai kashi a gindinsu, wanda EFCC da NJC ta fitar, ya nuna ya kamata a sallame su.

Sauran zarge-zarge kuma, aka mikawa kotu ta karasa.

Shi dai Alkalin, yana karyar cewa wai ba'a biya shi albashi ba, don haka yake amsar kudade daga lauyoyi da masu qara, da ma manyan kasar nan, saboda ya cika tumbinsa, binciken ya gano, ita kuma, kudaden aiki na ofis take kwashe wa.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel