Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa wasu 'yan bindiga dadi da ba'a san ko suwaye ba sun yi wa wata majami'a a garin Awka na jihar Anambra dirar mikiya inda kuma suka harbe faston cocin.

Kawo zuwa hada wannan labarin dai majiyar mu ta ce ba'a gama tantance ainihin halin da faston yake ciki ba biyo bayan kai shi wani boyayyen wuri da mabiyan sa sukayi.

Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya
Source: UGC

KU KARANTA: Yan bindiga sun harbe wani babban malami a Najeriya

Legit.ng dai ta samu lamarin dai ya faru ne da marece a garin na Awka dake zaman babban birnin jihar ta Anambra kuma kusa da ofishin 'yan sanda a unguwar da lamarin ya auku.

Wasu shaidun gani da ido dai sun ce 'yan bindigar wadanda har yanzu ba a san ainihin takamaiman dalilin aikata ta'asar ta su ba sun samu faston ne a kafafuwa da harbin bindigar tasu.

A wani labarin kuma, Wani dan majalisar wakilai a zauren majalisar taraya dake wakiltar mazabar Taura da Ringim a jihar Jigawa dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, Muhammad Gausu Boyi ya sha da kyar a hannun wasu mafusatan matasa.

Kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu, lamarin dai ya faru ne a garin Dutse dake zaman babban birnin jihar inda dan majalisar tare da wasu magoya bayan sa suka je domin tantance su a gabanin zabukan fitar da gwani da za'a gudanar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel