PDP ta kira taron gagawa yayin da ya rage kwanaki 2 ayi zaben cikin gida

PDP ta kira taron gagawa yayin da ya rage kwanaki 2 ayi zaben cikin gida

- Jam'iyyar PDP ta kira muhimmiyar taro da dukan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da za ayi a gobe Juma'a

- Ana sa ran za'a tattaunawa wasu muhimman abubuwa ne ciki har da za'a gudanar da babban taron jam'iyyar da duba jerin sunayen deliget

- Cikin wanda za su hallarci taron sun hada da dukkan masu neman takarar shugabancin kasa da 'yan kwamitin amintattu na jam'iyyar

A gobe Juma'a ne masu ruwa da tsaki a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za su gana da dukkan jiga-jigan jam'iyyar domin tattaunawa a kan batutuwa masu yawa musamman kan tsarin yadda za'a gudanar da babban taro na jam'iyyar.

Sanarwan taron ta fito ne daga bakin sakataren yada labarai na jam'iyyar, Mr. Kola Ologbondiyan a wata taron manema labarai da ya kira yau Alhamisa a babban birnin tarayya, Abuja.

PDP ta kira taron gagawa yayin da ya rage kwanaki 2 ayi zaben cikin gida

PDP ta kira taron gagawa yayin da ya rage kwanaki 2 ayi zaben cikin gida
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kwamishiniya a Gombe ta tika kawunta da kasa a zaben cikin gida na PDP

'Yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar da ake sa ran zasu hallarci taron sun hada da gwamna jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, gwamna Gombe, Ibrahim Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa.

Sauran sun hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Tanimu Turaki (SAN), tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi.

Sai kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da Dr Datti Baba-Ahmed.

Majiyar Legit.ng ta gano cewar abubuwan da za'a tattauna a taron sun hada da tsarin babban taron da kuma sake duba jerin sunayen deliget.

Shugaba jam'iyyar na kasa, Uche Secondus ne zai jagoranci gudanar da taron da ake sa ran kwamitin amintattu da sauran bangarori na jam'iyyar duk za su hallarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel