Wata daban: Manyan jami'an hukumar tsaro ta DSS na shirin kawowa tazarcen Buhari cikas

Wata daban: Manyan jami'an hukumar tsaro ta DSS na shirin kawowa tazarcen Buhari cikas

Nadin Yusuf Magaji Bichi da shugaba Buhari ya yi a matsayin sabon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ya bar baya da kura tare da jawo guna-guni a tsakanin manyan darektocin hukumar.

A yanzu dai wasu daga cikin manyan jami'an hukumar DSS da nadin Bichi bai yiwa dadi ba, na kulle-kullen ganin yadda zasu yi amfani da karfin su tare da gogewarsu ta aiki wajen ganin sun yiwa yunkurin Buhari na tazarce kafar ungulu tare da lalata duk wani yunkuri na kawo karshen yaki da Boko da gwamnatin ta Buhari ke yi.

A ranar 13 ga watan Satumba ne Bichi ya karbi aiki daga hannun shugaban DSS na rikon kwarya, Matthew Seiyefa, mutumin da ya zama shugaba a hukumar bayan Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki.

Tarnaki: Manyan jami'an hukumar tsaro ta DSS na kulle-kullen kifar da gwamnatin Buhari

Tarnaki: Manyan jami'an hukumar tsaro ta DSS na kulle-kullen kifar da gwamnatin Buhari

Wanna sa-toka-sa-katsi dake faruwa a hukumar ta DSS na kunshe ne cikin wani rahoto na jarida Premium Times da Legit.ng ta ci karo da shi a yau, Alhamis, 4 ga watan Oktoba.

DUBA WANNAN: Dalibin Jami'ar ABU ya kera jirgin yaki, ya saka masa suna 'mai ceton 'yan matan Chibok'

Manyan jami'an DSS dake shelkwatar su dake Abuja da abokanan aikinsu dake jihohi sun fusata da nadin Bichi ne saboda ganin cewar ya riga ya yi ritaya amma shugaba Buhari ya zabi dawo da shi bayan ga su a cikin aiki har yanzu.

Wadannan jami'ai, wasun su daga arewa, na ganin shugaba Buhari bai yi masu adalci ba tare da yin tambayar, "mu kenan ba zamu taba shugabantar hukumar ba?".

Jaridar Premium Times ta bayyana cewar wasu jami'an DSS sun shaida mata cewar hatta cire Seiyefa da Buhari ya yi, akwai hannun wasu na kusa da shi da basu ji dadin cire Daura da Osinbajo ya yi ba, musamman ganin yadda shi Seiyefa ya fara nuna masu alamun ba zai yi aiki bisa son rai ba.

Premium Times ta ce, a wani binciki da ta gudanar, shugaba Buhari da kansa ya san yana fuskantar tarnaki daga jami'an tsaro a kudirinsa na yin tazarce.

Manyan jami'an hukumar DSS sun shaidawa Premium Times din cewar ba zasu taba yafewa Buhari kuma sun gwammaci taimakawa jam'iyyar adawa a kan su taimaki Buhari ya kara cin zabe a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel