Ta tabbata Atiku ne zai iya karawa da Buhari a 2019 - Sakamakon zaben yanar gizo

Ta tabbata Atiku ne zai iya karawa da Buhari a 2019 - Sakamakon zaben yanar gizo

- Alkaluma sun nuna cewa Atiku Abubakar, ne kadai zai iya karawa da shugaban kasar Muhammadu Buhari a zaben 2019

- An samu alkaluman ne daga sakamakon wani zabe a yanar gizo da shafin jam'iyyar PDP na jihar Rivers (@PDP_RIVERS) ya gudanar

- A karshen zaben ranar Alhamis, Atiku ya samu kaso 48 na gaba daya kuri'un da aka kada, sai Saraki ke binsa da kaso 37

Alkaluma sun nuna cewa tsohon shugaban kasar Nigeria kuma mai son tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ne kadai zai iya karawa da shugaban kasar yanzu Muhammadu Buhari a babban zaben 2019.

Alkaluman da aka samu daga sakamakon wani zabe a yanar gizo da shafin jam'iyyar PDP na jihar Rivers (@PDP_RIVERS) ya gudanar, ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya doke shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, inda ya zo na daya a zaben.

A karshen zaben ranar Alhamis, Atiku ya samu kaso 48 na gaba daya kuri'un da aka kada, sai Saraki ke binsa da kaso 37, Kwankwaso kaso 11, yayin da Tambuwal ya zo na karshe da kaso 4 kacal.

KARANTA WANNAN: Buhari na amfani da hukumomin tsaro don gallazawa kabilu - Jigon ACF

Ta tabbata Atiku ne zai iya karawa da Buhari a 2019 - Sakamakon zaben yanar gizo

Ta tabbata Atiku ne zai iya karawa da Buhari a 2019 - Sakamakon zaben yanar gizo
Source: Depositphotos

Mutane 41,734 ne suka kad'a kuri'a a zaben cikin kwanaki 6 wanda ya fara tun a ranar 29 ga watan Satumba, aka kammala a yammacin ranar 4 ga watan Oktoba, 2018.

Atiku ya samu jimillar kuri'u 20,032 idan aka alakanta shi da Saraki mai kuri'u 15,442, kwankwaso mai kuri'u 4,591, ya yinda shi Tambuwal ya tashi da sauran kuri'u 1, 669.

A zaben, an tambayi masu kad'a kuri'ar; "An gama tabbatar da komai na cewa jam'iyyar PDP za ta gudanar da zaben fitar da gwani a jihar Rivers a ranar 6 ga watan Oktoba. Wa kuke tunanin ya cancanci ya kara da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaza, a zaben 2019?." An bada zabi tsakanin Atiku, Saraki, da Tambuwal Kwankwaso.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel