Tanadin da na yi wa Najeriya idan na zama shugaban kasa - Tambuwal

Tanadin da na yi wa Najeriya idan na zama shugaban kasa - Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peroples Democratic Party (PDP), Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa zai sauya fasalin lamuran kasar nan idan har yayi nasarar zama shugaban kasa a zaben 2019.

Tambuwal ya bayyana hakan a yayinda da ya ke jawabi ga taron ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Lagas, a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba.

Kamfanin Dillancin Najeriya ya ruwaito cewa ziyarar da ya kai wa jam’iyyar a Lagas na daga cikin rangadin neman goyon bayan ‘yaýan jam’iyyar da yake yi a fadin kasar gabannin zaben fidda gwani da za’a gudanar a karshen mako.

Tanadin da na yi wa Najeriya idan na zama shugaban kasa - Tambuwal

Tanadin da na yi wa Najeriya idan na zama shugaban kasa - Tambuwal
Source: Facebook

Ya ce a shirye ya ke karfafa tare da daukaka kima da martabar tattalin arzikin kasar nan yadda Najeriya za ta samu bunkasa , domin ya na da gogewar sanin makamar shugabanci.

KU KARANA KUMA: Kwastam sun kama wata mota cike da kayan sojoji

Ya kara da cewa Najeriya na fuskantar gagarumar kalubale na tattalin arziki da kuma tsaro da ke bukatar shugaban da zai iya kawo mafita mai dorewa cikin dan lokaci kalilan.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba yace gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne domin neman mafita ga rikicin da ya kunno kai a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Okorocha ya kasance daya daga cikin gwamnonin dake fuskantar matsaloli a jiharsa saboda hukuncinsa na goyon bayan surikinsa, Uche Nwosu, don ganin yayi nasara.

Ya jagoranci takwarorinsa bakwai don ganawa da Shugaba Buhari a ofishinsa a ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel