Buhari na amfani da hukumomin tsaro don gallazawa kabilu - Jigon ACF

Buhari na amfani da hukumomin tsaro don gallazawa kabilu - Jigon ACF

- Mohammed Abdulrahman, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na amfani da hukumomin tsaro don gallazawa kabilu

- Ya ce Ubangiji ya baiwa Buhari ragamar mulkin Nigeria amma ya cire masa ilimin sanin ko zai hidimtawa jama'ar kasar ko akasin hakan

- Ya ce Nigeria nada akalla kabilu 370. Sune ke da iko kan kasar, ba wai 'yan Arewa ko wata kabila guda daya ba

Mamba a kwamitin zartaswa na kungiyar 'yan Arewa ACF, Mohammed Abdulrahman, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya cimma kawo dai-daito a bangaren nadin mukaman shuwagabannin tsaro na kasar kafin 2019 ba.

Mohammed Abdulrahman a zantawarsa da kamfanin jarida na Punch, ya ce abun takaici ne yadda gwamnati ta zuba idanuwa tana nazarin abubuwan da ke wakana a kafafen sada zumunta na zamani yayin da ake kashe mutane tare da zubar da jinin wadanda basu ji ba basu gani ba a fadin kasar.

Ya ce Ubangiji ya baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ragamar mulkin Nigeria amma ya cire masa ilimin sanin ko zai hidimtawa jama'ar kasar ko akasin hakan, "saboda canja fasalin kasar da daga darajar kasar a idon Afrika da duniya baki daya Allah ya ba shi mulki. Sai dai a maimakon hakan, sai ma kara tabarbarar da komai yayi."

KARANTA WANNAN: Ambaliyar ruwa: Za a fuskanci karancin shinkafa a shekara mai zuwa a Nigeria - Ogbeh

Buhari na amfani da hukumomin tsaro don gallazawa kabilu - Jigon ACF

Buhari na amfani da hukumomin tsaro don gallazawa kabilu - Jigon ACF
Source: Depositphotos

Sai dai ya ce duk abubuwan da mutum zai yi ance ya rinka sara yana duban bakin gatari. "Duk da irin karfin iko da tsaro da shugaban kasar ke amfani da shi don tarwatsa jama'a mai karewa ne, yanzu ya bar batun mulki kwata kwata, amma Allah na kallo kuma zai yi hisabi.

Ko da aka tambayi Abdullahi dangane da tsarin nadin shuwagabannin tsaro daga kabilun kasar, ya ce: "Ai abunda na ke nuna maku kenan, a Nigeria muna da akalla kabilu 370. Sune ke da iko kan kasar, ba wai 'yan Arewa ba "

Haka zalika jigon kungiyar ACF ya ce babu ta yadda za ayi shugaban kasa Buhar ya dai-daita tsarin nadin shuwagabannin tsaro na kasar kafin 2019, "idan ma ya iya canjawa, to ba zai yi hakan don ci gaban kasar ba. Amma zaben 2019 na zuwa, kowa zai gani a kwaryar cin tuwonsa."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel