Dalilin ganawarmu da Buhari - Rochas

Dalilin ganawarmu da Buhari - Rochas

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba yace gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne domin neman mafita ga rikicin da ya kunno kai a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Okorocha ya kasance daya daga cikin gwamnonin dake fuskantar matsaloli a jiharsa saboda hukuncinsa na goyon bayan surikinsa, Uche Nwosu, don ganin yayi nasara.

Ya jagoranci takwarorinsa bakwai don ganawa da Shugaba Buhari a ofishinsa a ranar Alhamis.

Dalilin ganawarmu da Buhari - Rochas

Dalilin ganawarmu da Buhari - Rochas
Source: UGC

Sun kwashe tsawo sa’a guda suna ganawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Oshiomhole na ganawa mai muhimmanci da gwamnonin APC

Da yake Magana ga manema labarai a fadar shugaban kasa, Okorocha ya bayyana cewa sun je villa ne domin “sake duba rikice-rikice dake kewaye da zaben fidda gwaninmu musamman a APC domin samun mafita.”

Gwamnan yace sun gana da Buhari domin sanin matakin dauka kan rikicin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel