Yanzu-Yanzu: 'Yan shi'a sun garkame wata babbar kotu a Abuja har sai an sako jagoran su

Yanzu-Yanzu: 'Yan shi'a sun garkame wata babbar kotu a Abuja har sai an sako jagoran su

- 'Yan shi'a sun garkame wata babbar kotu a Kaduna

- Sun ce ba za su bude ta ba har sai an sako jagoran su

- Alkalin kotun ya dage karar shi kuma

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa daruruwan mabiya darikar Shi'a karkashin jagorancin malamin su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suna gudanar da wata kwarya-kwaryar zanga-zanga a gaban wata babbar kotun garin Abuja.

Yanzu-Yanzu: 'Yan shi'a sun garkame wata babbar kotu a Kaduna har sai an sako jagoran su

Yanzu-Yanzu: 'Yan shi'a sun garkame wata babbar kotu a Kaduna har sai an sako jagoran su
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An gano kasuwar jarirai a Najeriya

Haka zalika mun samu cewa mabiya shi'ar sun garkame kofar shiga kotun da kwado inda suka ce ba za su bude ba har sai kotun ta bayar da umurnin a saki jagoran na su dake a tsare sama da kwanaki 1000.

Legit.ng ta samu cewa tun farko dai babbar kotun a jihar Kaduna ta sake daga karar shugaban kungiyar mabiya Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, da uwargidarsa, Zeenat El-Zakzaky zuwa ranan 7 ga watan Nuwamba, 2018.

Alkali mai Shari’a, Justice Gideon Kurada, ya daga wannan karar ne bisa ga korafin lauyan gwamnati, Dari Bayero, kan rashin tsaro a jihar Kaduna.

Lauyan gwamnatin ya bayyana cewa hukumar yan sandan jihar ta tura dukkan jami’an tsaronsu wurare daban-daban domin ziyarar mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, zuwa Kaduna yau.

Dukkan lauyoyin sun amince da wannan bukata saboda babu isassun jami’an tsaron da zasu tsare kotun.

A wani labarin kuma, Wasu takardaun tarukan sirri da bamu kai ga tabbatar da sahihancin su na zaman taron da 'yan kabilar Birom dake a jihar Filato suka gudanar akan musulmai da 'yan kabilar Hausawa, fulani, Inyamurai da dai sauran su sun bulla a saman yanar gizo.

Takardun na zaman wanda aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuni na shekarar 2010 mun samu cewa ya samu halartar mutane da dama 'yan asalin kabilar ta Birom ciki hadda gwamnan jihar a wancan lokacin, Sanata Jonah David Jang da wasu mukarraban gwamnatin sa da dama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel