Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna, hotuna

Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna, hotuna

A yau, Alhamis, ne mataimakin shugaban shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci jihar Kaduna domin kaddamar da shirin bayar da tallafin kudi ga kananan 'yan kasuwa.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ne ya tarbi Osinbajo bayan ya isa garin Kaduna da safiyar yau.

Kafin kaddamar da shirin rabon tallafin kudi ga kananan 'yan kasuwar, Osinbajo ya ziyarci wata cibiyar koyar da sana'o'i ga matasa da gwamnatin jihar Kaduna ta samar.

El-Rufa'i da Osinbajo sun duba wasu daga cikin irin kayayyakin da cibiyar koyawa matasa sana'o'in ta samar. An yi wannan bajakolin ne a dakin taro na Umaru Musa Yar'adua dake cikin garin Kaduna.

Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna, hotuna

Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna
Source: Twitter

Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna, hotuna

Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna
Source: Twitter

Kazalika, Osinbajo ya gabatar da kyaututtuka ga wasu hazikan matasa da suka yi bajinta a shirin da jihar Kaduna ta gudanar na koyawa matasa sana'o'in dogaro da kai kafin basu jari.

Har ila yau, Osinbajo ya kara ziyartar wata cibiyar bawa matasa ilimin na'ura mai kwakwalwa (KADHUB) da gwamnatin jihar Kaduna ta samar.

DUBA WANNAN: Zaben cikin gida: An yi takara tsakanin uwa da 'da a jam'iyyar APC

Bayan ziyarar KADHUB ne sai sai Osinbajo da El-Rufa'i suka rankaya zuwa babbar kasuwar garin Kaduna domin gabatar da shirin gwamnatin tarayya na raba jarin 10,000 ga kananan 'yan kasuwa.

Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna, hotuna

Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna
Source: Twitter

Osinbajo ya raba kyauta ga hazikan matasa a Kaduna, hotuna

Osinbajo, El-Rufa'i da hazikan matasa
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel