Da dumin sa: Shugaba Buhari yayi sabon nadi mai muhimmaci a hukumar EFCC

Da dumin sa: Shugaba Buhari yayi sabon nadi mai muhimmaci a hukumar EFCC

- Shugaba Buhari yayi sabon nadi mai muhimmaci a hukumar EFCC

- Shugaba Buhari ya nada Sabon sakatare na hukumar EFCC

- Tuni ya aikawa da Saraki wasikar hakan

Shugaban kasar tarayyar Najeriya a rubutawa majalisar dattawan Najeriya takarda zuwa ga Saraki yana neman amincewar su game da wani sabon nadi da yayi a hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance.

Da dumin sa: Shugaba Buhari yayi sabon nadi mai muhimmaci a hukumar EFCC

Da dumin sa: Shugaba Buhari yayi sabon nadi mai muhimmaci a hukumar EFCC
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An kama manyan matsafa 13 a Arewa

Mun samu cewa dai shugaban kasar ya tura sunan Mista Olanipekun Olukoyede a matsayin Sakataren hukumar ta EFCC inda yake neman su tantance shi.

Legit.ng ta samu cewa shi dai Mista Olanipekun Olukoyede yanzu haka shine shugaban ma'aikata na shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu kuma kwararre ne sosai.

A wani labarin kuma, Akalla gwamnoni hudu ne kawo yanzu suka fito fili suka wasa wukar su domin shiga yaki gadan-gadan da shugaban jam'iyya mai mulki ta APC, Kwamared Adams Oshiomhole game da zabukar fitar da gwani da ake yi yanzu haka.

Gwamnonin da muka samu labarin sun soma yin fito-na-fito da shugaban jam'iyyar dai sune Abdulaziz Yari na jihar Zamfara; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo; Nasir El-Rufai daga Kaduna da kuma Ibikunle Amosun daga jihar Ogun.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel