Zaben 2019: Dattijan shiyyar Shugaba Buhari sun marawa Makarfi baya

Zaben 2019: Dattijan shiyyar Shugaba Buhari sun marawa Makarfi baya

- Dattijan shiyyar Shugaba Buhari sun marawa Makarfi baya

- Sun ce dattakun shi da kwarewa ta sa suka yanke wannan hukuncin

- Sun kuma fadi dalilin da ya sa ba za su zabi Sule Lamido ba

Jiga-jigan 'yan siyasa da kuma dattijai masu fada aji daga shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga cikin ta sun lashi takobin marawa Sanata Ahmad Makarfi baya a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP da ke tafe.

Zaben 2019: Dattijan shiyyar Shugaba Buhari sun marawa Makarfi baya

Zaben 2019: Dattijan shiyyar Shugaba Buhari sun marawa Makarfi baya
Source: Twitter

KU KARANTA: An umurci jami'an tsaro su kawo karshen rikicin Filato

Da suke bayyana dalilin su na yin hakan, dattijan da 'yan siyasar a karkashin inuwar kungiyar North West Progressives Forum (NWPF) sun bayyana cewa kyawawan manufofi da kudurorin sa ne suka sa su yanke wannan shawarar.

Legit.ng ta samu cewa mai magana da yawun su Isa Saleh Funtua haka zalika ya bayyana cewa duba da yadda suka fi kowane yanki a Najeriya yawan masu zabe, wannan ba karamar nasara bace ga dan takarar nasu.

Ya kara da cewa duk da sun tattauna sosai a zaman su game da marawa Dakta Sule Lamido baya, amma hakan ba zai yiwuba duba da shari'ar cin hanci da rashawa da yake fuskanta yanzu haka a gaban kotu.

A wani labarin kuma, Akalla gwamnoni hudu ne kawo yanzu suka fito fili suka wasa wukar su domin shiga yaki gadan-gadan da shugaban jam'iyya mai mulki ta APC, Kwamared Adams Oshiomhole game da zabukar fitar da gwani da ake yi yanzu haka.

Gwamnonin da muka samu labarin sun soma yin fito-na-fito da shugaban jam'iyyar dai sune Abdulaziz Yari na jihar Zamfara; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo; Nasir El-Rufai daga Kaduna da kuma Ibikunle Amosun daga jihar Ogun.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewarku tare da mu

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel