Kwastam sun kama wata mota cike da kayan sojoji

Kwastam sun kama wata mota cike da kayan sojoji

- Kwastam sun kama wata motar bas dauke da buhu biyu dake cike da kayan sojoji da takalmansu

- Bus din da aka kama mallakar kamfanin Chimezie Motors Nigeria Limited ne

- An kama su ne a yankin Ijebu-Ode a ranar laraba

Hukumar kwastam na Najeriya dake aiki a sashin Zone ‘A’ sun kama wata motar bas dauke da buhu biyu dake cike da kayan sojoji da takalmansu a hanyar babban titin Ijebu-Ode.

An kama bus din kirar Hiace wanda yake mallakar kamfanin Chimezie Motors Nigeria Limited da lamba: JJT 905 XB a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba.

Kwastam sun kama wata mota cike da kayan sojoji

Kwastam sun kama wata mota cike da kayan sojoji
Source: Facebook

Mohammed Aliyu, shugaban kwastam na sashin, ya fadama manema labarai a Lagas a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba cewa an kama kayan ne bayan tsegumi da jami’an tsaro suka samu daga ‘yan Najeriya masu kishin kasa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta rabawa mutane 10,490 Naira miliyan 210 a jihar Kaduna

Bayan haka ya sanar da cewa sun kama manyan motoci na alfarma guda hudu da kuma buhuhunan shinkafa duk a bakin aiki.

A wani lamari na daban Legit.ng ta rahoto cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a karamar hukumar Demsa da ke jihar Adamawa a ranar Talata yayin da ake gudanar da taron sulhu da makiyaya inda suka kashe mutum guda daya.

Mai magana da yawun Fulani, Usman Ali, ya shaidawa manema labarai jiya a Yola cewar an kaiwa wasu Fulani hari yayin da suke wata zaman sulhu da Basaraken Bata, Hama Bata, Ahmadu Teneke ya shirya.

Ali ya ce a kwanakin baya wasu 'yan bindigan sun kashewa Fulani shanu 20 ba tare da watta hujja ba hakan yasa 'yan kungiyar suka kai kara ofishin 'yan sanda da ke garin Demsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel