Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu

- Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Thabo Mbeki ya ziyarci Buhari

- Ya ziyarci shugaban kasar ne a fadarsa dake Abuja

A ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Thabo Mbeki.

Shugabannin kasashen biyu sun gana ne a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

Mbeki ya isa fadar Villa da misalin karfe 2:30 na rana sannan aka yi masa jagora zuwa ofishin Shugaba Buhari.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter.

Mbeki na daya daga cikin shugabannin Afrika da suka ziyarci Shugaba Buhari a 2018.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, na ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a ofishinsa dake fadar shugaban kasa Aso Villa.

Daga cikin gwamnonin da ke halarce sune gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari; gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha; gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Shettima ya lashe tikitin takarar sanata a APC

Sauran sune gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Plateau, gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanko AlMakura da gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel