Gwamnatin Buhari ta rabawa mutane 10,490 Naira miliyan 210 a jihar Kaduna

Gwamnatin Buhari ta rabawa mutane 10,490 Naira miliyan 210 a jihar Kaduna

- Gwamnatin tarayya ta raba akalla Naira miliyan 210 ga mutane 10,490 da ke da karamin karfi a jihar Kaduna

- Zailani ya bayyana cewa wadanda suka ci gajiyar wannan tallafin, sun fito ne daga kananan hukumo 9 na jihar

- A cewar sa, an fara raba N5,000 ga wadanda suka ci gajiyar shirin ne a cikin watan Fabreru

Gwamnatin tarayya ta raba akalla Naira miliyan 210 ga mutane 10,490 da ke da karamin karfi da kuma marasa galihu a jihar Kaduna karkashin shirin 'Condition Cash Transfer', wanda gwamnatin ta bullo da shi don rage talauci a fadin kasar.

A ranar Alhamis, Alhaji Mahmoud Zailani, babban sakataren ma'aikatar bunkasa karkara da al'umomi ta jihar, ya bayyana hakan a wata sanarwa wacce aka samawa manema labarai a Kaduna, cikinsu kuwa harda Legit.ng.

Zailani ya bayyana cewa wadanda suka ci gajiyar wannan tallafin, sun fito ne daga kananan hukumo 9 na jihar da suka karbar N5,000 na watan Fabreru, Mayu, Afreul da kuma watan Mayu.

KARANTA WANNAN: Karshen alewa: Kotu ta garkame wani mutumi bayan kama shi da laifin kashe kaninsa

Gwamnatin Buhari ta rabawa mutane 10,490 Naira miliyan 210 a jihar Kaduna

Gwamnatin Buhari ta rabawa mutane 10,490 Naira miliyan 210 a jihar Kaduna
Source: Depositphotos

Ya zayyana kananan hukumomin da suka hada da Ikara, Kubau, Lere, Birnin Gwari, Chikun, Kajuru, Kachia, Kauru da kuma karamar hukumar Sanga.

A cewar sa, sashen shirin na jihar Kaduna, da ke a cikin ma'aikatar ya fara raba N5,000 ga wadanda suka ci gajiyar shirin ne a cikin watan Fabreru.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya fitar da rahoton cewa wannan shirin na gudana ne karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma shiri gwamnatin tarayya na bunkasa rayuwar jama'a wanda aka samar da shi a 2016 don dakile rashin aikin yi, talauci da kuma tamowa a kasar.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel