An daga karar El-Zakzaky saboda rashin isasshen tsaro a Kaduna

An daga karar El-Zakzaky saboda rashin isasshen tsaro a Kaduna

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta sake daga karar shugaban kungiyar mabiya Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, da uwargidarsa, Zeenat El-Zakzaky zuwa ranan 7 ga watan Nuwamba, 2018.

Alkali mai Shari’a, Justice Gideon Kurada, ya daga wannan karar ne bisa ga korafin lauyan gwamnati, Dari Bayero, kan rashin tsaro a jihar Kaduna.

Lauyan gwamnatin ya bayyana cewa hukumar yan sandan jihar ta tura dukkan jami’an tsaronsu wurare daban-daban domin ziyarar mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, zuwa Kaduna yau.

Dukkan lauyoyin sun amince da wannan bukata saboda babu isassun jami’an tsaron da zasu tsare kotun.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnonin APC 8 na ganawa da Buhari kan Oshiomole

A bangar guda, Bayero ya bayyanawa manema labarai cewa har yanzu ba’a damke wasu yan Shi’a biyu da ake zargi masu suna Yakubu Yakaya da Sanusi Abdulqadir.

Mun kawo muku rahoton Babban kotun jihar Kaduna za ta yanke hukunci kan bukatan belin da shugaban kungiyar mabiya kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wanda akafi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da uwargidarsa suka gabatar a gaban kotu.

Babban alkalin kotun, Jastis Gideon Kurada, ya daga karan zuwa yau 4 ga watan Oktoba, daga ranan 2 ga watan Agusta domin ganin yiwuwan bashi beli bayan kimanin shekaru uku a tsare.

Ana gurfanar da shugaban kungiyar Shi’an ne bisa ga laifin kokarin haddasa fitina a kasa, tayar da tarzoma, da sauransu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Legit.ng Hausa zata koma LEGIT.ng Hausa, wannan babban cigaba ne

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel