Hadimin Buhari ya fadi zaben fidda gwani na sanatoci

Hadimin Buhari ya fadi zaben fidda gwani na sanatoci

Hadimin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Kawu Sumaila ya fadi zaben fidda gwani na neman kujerar sanata na yankin Kano ta Kudu a karkashin jam’iyyar All Progressive Congress (APC).

Sanata Kabiru Gaya, tsohon gwamnan jihar Kano ne ya lashe tikitin a ranar Talata, 2 ga watan Oktoba.

Gaya ya samu kuri’u miliyan daya a zaben fidda gwanin da aka gudanar a fadin yankin a ranar Talata da ya gabata.

Hadimin Buhari ya fadi zaben fidda gwani na sanatoci

Hadimin Buhari ya fadi zaben fidda gwani na sanatoci
Source: UGC

Da yake sana da sakamakon zaben a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba, jami’in zaben, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada yace Gaya ya samu kuri’u 1,357,000 inda ya kayar da hadimin shugaban kasar wanda ya samu kuri’u 309,209.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima, ya mallaki tikitin takarar kujerar sanata na yankin Borno ta tsakiya karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa

Yayi nasara a zaben fidda gwani wanda aka gabatar a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba wanda aka sanar da sakamakon a safiyar yau Alhamis, 4 ga watan Oktoba.

Ya samu kuri’u 2,735 inda ya doge abokin takararsa Alhaji Ali Wurge wanda ya samu kuri’u biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel