Hukumar EFCC ta gurfanar da Hadimin Saraki kan Zambar N3.5b

Hukumar EFCC ta gurfanar da Hadimin Saraki kan Zambar N3.5b

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta gurfanar da Gbenga Makanjuola, hadimin shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, a gaban babbar kotun jihar Legas bisa aikata laifin zamba.

Ana zargin babban hadimin na Saraki tare da wasu mutane uku da aikata laifin zambar makudan dukiya ta kimanin N3.5b, inda suka gurfanar gaban alkalin kotun, Babs Kuewumi.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ana zargin wannan Mutane hudu ta kulla tuggun wannan zamba ta hanyar amfani da asusun banki mallakin wani kamfani, Melrose General Services Limited, wajen wawuson wannan makudan dukiya.

Wannan laifi ya sabawa sashe na 15 cikin dokokin da suka shafi harkokin kudi na Najeriya kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Hadimin Saraki kan Zambar N3.5b

Hukumar EFCC ta gurfanar da Hadimin Saraki kan Zambar N3.5b
Source: Depositphotos

Lauyan hukumar, Mista Ekene Iheanacho, ya roki kotun akan ta bayar da umarnin tsare wadanda ake zargi kafin ta kammala binciken domin zartar ma su da hukuncin da ya daidai da abinda suka aikata.

KARANTA KUMA: Ba zan bari a Kunyata Najeriya ba - Buhari

A sanadiyar haka alkali Kuewumi ya daga sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Okotoba kamar yadda shafin jaridar ta The Nation ta bayyana.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yayin da zaben 2019 ke ci gaba da karatowa, rikici ya kunno kai tsakanin gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel