2019: Rikici ya kunno kai tsakanin gwamnonin APC da Adams Oshiomole

2019: Rikici ya kunno kai tsakanin gwamnonin APC da Adams Oshiomole

Wata sabuwar rikici ta kunno kai shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da akalla gwamnonin jam’iyyar hudu yayinda suke shirin fito na fito da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole.

Gwamnonin sune: Abdulaziz Yari na jihar Zamfara; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo; Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da Ibikunle Amosun na jihar Ogun. Suna rikici ne kan yunkurin da jam’iyyar keyi na baiwa wasu sanatoci tikitin kai tsaye na takara ba tare da yin zaben fid da gwani ba.

Gwamnonin sun fara zargin shugaba jam’iyyar ta shugabannin jam’iyyun ta jiha kan kokarin yi musu kama karya wajen zaben yan takara.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun mamaye titunan Kaduna yayinda za’a gurfanar da El-Zakzaky, da yiwuwan a bashi beli

A ranan Talata, shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, ya saki jerin sunayen yan takaran da jam’iyyar ta tantance domin takara. A wannan jadawali, an cire sunayen wadansu yan takara domin baiwa wasu daman takara su kadai saboda suna masa biyayya.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Kaduna, Naisr Ahmed El-Rufa’I da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, sun shiga ganawar sirri da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ta Aso Rock, Abuja.

Gwamnonin biyu sun isa fadar shugaban kasan ne misalin karfe 3:15 na rana. ba mu samu rahoton abinda suka tattauna ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Legit.ng Hausa zata koma LEGIT.ng Hausa, wannan babban cigaba ne

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel