Jami’an tsaro sun mamaye titunan Kaduna yayinda za’a gurfanar da El-Zakzaky, da yiwuwan a bashi beli

Jami’an tsaro sun mamaye titunan Kaduna yayinda za’a gurfanar da El-Zakzaky, da yiwuwan a bashi beli

Babban kotun jihar Kaduna za ta yanke hukunci kan bukatan belin da shugaban kungiyar mabiya kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wanda akafi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da uwargidarsa suka gabatar a gaban kotu.

Babban alkalin kotun, Jastis Gideon Kurada, ya daga karan zuwa yau 4 ga watan Oktoba, daga ranan 2 ga watan Agusta domin ganin yiwuwan bashi beli bayan kimanin shekaru uku a tsare.

Ana gurfanar da shugaban kungiyar Shi’an ne bisa ga laifin kokarin haddasa fitina a kasa, tayar da tarzoma, da sauransu.

An fara gurfanar da su ne ranan 15 ga watan Mayu 2018 bayan garkameshi a watan Disamban 2015 a Zaria.

Gabanin gurfanar da isa a yau, jami’an tsaro sun tare dukkan hanyoyin da ya nufi kotun. Babu wanda aka baiwa daman wucewa tamkar yan jarida.

Hukumar ta dau wannan mataki ne bisa ga rikicin da ya faru kwanakin bayan tsakanin mabiya Sheik Zakzaky da jami’an yan sanda wanda ya kai ga hallakan jami’I dan sanda daya.

Zamu kawo muku cikakken rahoton...

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel