Gwamna Al-Makura ya yi nasarar samun tikitin APC na tsayawa takarar sanata a Nasarawa

Gwamna Al-Makura ya yi nasarar samun tikitin APC na tsayawa takarar sanata a Nasarawa

An zabi Gwamna Umaru Al-Makura a matsayin dan takarar kujeran sanata na Nasarawa ta kudu a zaben 2019 karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Shugaban kwamitin zaben, Ismaila Ahmed, wanda ya samu wakilcin sakataren, Abdullahi Candido ya sanar da sakamakon zaben a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba, a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Ahmed yace Al-Makura ya samu kuri’u 1,262 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Sanata Salisu Egyegbola, wanda ya samu kuri’u 312.

Gwamna Al-Makura ya yi nasarar samun tikitin APC na tsayawa takarar sanata a Nasarawa

Gwamna Al-Makura ya yi nasarar samun tikitin APC na tsayawa takarar sanata a Nasarawa
Source: Twitter

Yayi bayanin cewa wakilai 1,612 ne aka sanya ran zasu yi zaben, an tantance 1,608 yayinda 1,5994 suka yi zabe. 20 sun langwala ba daidai ba.

A halin da ake ciki, Al-Makura ya nuna farin ciki kan sakamakon saben sannan ya sadaukar da nasarar ga mutanen jihar.

KU KARANTA KUMA: Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa

Ya kuma yaba da dattakon abokin hamayyarsa da ya amshi sakamakon zaben da zuciya daya. Ya kuma yaba ma kwamitin zaben bisa adalci da suka yi shirin, cewa sun nuna lallai su masu gaskiya ne a APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel