Karshen alewa: Kotu ta garkame wani mutumi bayan kama shi da laifin kashe kaninsa

Karshen alewa: Kotu ta garkame wani mutumi bayan kama shi da laifin kashe kaninsa

- Kotu ta garkame wani matashi mai shekaru 28, Collins Abakwe a gidan kaso na tsawon shekaru 10 sakamakon kashe kaninsa

- Ya aikata kisan ne a shekara ta 2013 bayan da ya yi cacar-baki da kanin nasa akan budurwa

- Ya kashe kanin nasa, Chibuike a gida mai lamba 54, layin Adeyanju, Amukoko jihar Legas

A ranar Laraba, wata babbar kotu a Ikeja ta garkame wani matashi mai shekaru 28, Collins Abakwe a gidan kaso na tsawon shekaru 10, sakamakon kama shi da laifin kashe kaninsa mai suna Chibuike Abakwe, bayan sun yi musayar yawu akan wata budurwa.

Mai shari'a Raliat Adebiyi ta yanke wannan hukuncin ga wanda ake zargin, wanda aka gabatar da shi a gaban bisa aikata laifin kisan kai a 2013, bayan da kuma kotun ta same shi dumu-dumu da aikata wannan laifin na kisan kai.

Da farko an fara zargin sa da cewar ya dauki hukunci a hannunsa na kashe mutum, ba tare da wasu dalilai da suka cancanci kisan ba, bayan kuma sa-insar da Collin ya yi da jihar a waccen shekarar.

KARANTA WANNAN: Rikicin Jos: Buratai ya zargi masu madafun iko da haddasa rikicin bayan cafke mutane 73

Karshen alewa: Kotu ta garkame wani mutumi bayan kama shi da laifin kashe kaninsa

Karshen alewa: Kotu ta garkame wani mutumi bayan kama shi da laifin kashe kaninsa
Source: Depositphotos

Adebiyi ta ce ta ce kotun ta amince da wannan hukunci da majalisar zartaswar shari'a da kuma masu shigar da karar suka yanke. Don haka ne kotun ta yankewa wanda ake tuhumar hukuncin shekaru 10 a gidan kaso.

Kafin yanke masa wannan hukuncin, Adebiyi ta tambayi Collins ko ya fahimci wannan hukunci da kotun ta ke zartaswa akanshin da kuma yarjejeniyar da ya shiga. Collins, ya bata tabbacin ya fahimci komai tunda shine ya sa hannu akan yarjejeniyar.

A cewar Mrs O. A. Olugasa, shugabar masu shigar da kara daga bangaren jihar, ta bayyana cewa Collins ya aikata laifin ne a ranar masoya ta duniya na 2013, a gida mai lamba 54, layin Adeyanju, Amukoko jihar Legas.

"Collin ya dabawa kaninsa, Chibuike fasassar, wanda hakan ya zama silar mutuwarsa a yayin da suke musayar yawu. Yan uwan suna gardamar ne akan wata budurwar abokinsu, wacce ake takaddamar kwananta a cikin gidan nasu."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel