Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa

Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa

Yan takarar kujeran majalisar dokoki na kasa daga jihar Ondo a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wadanda aka hana yin zaben fidda gwani na jam’iyyar a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba sun yi kira ga Mista Adams Oshiuomhole da yayi murabus daga matsayinsa na shugaban jam’iyyar na kasa.

A cewar yan takarar, Oshiomhole bai cancanci jagorancin jam’iyyar ba.

Da yake Magana a madadin sauran yan takarar a wani taron manema labarai a Akure, babban birnin jihar Ondo, Dr Tunji Abayomi yace Oshiomhole baida karfin jagorantar jam’iyyar, cewa yana ta kore ra’ayoyin jama’a tun bayan da ya hau matsayin shugaban jam’iyyar.

Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa

Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa
Source: Depositphotos

A cewar Abayomi, hana su da akayi ya saba ma kundin tsarin jam’iyyar da ma na kasa baki daya.

Ya kuma bayyana matakan jam’iyyar a matsayin rashin adallci a gare su tunda hart a hana su shiga takarar.

KU KARANTA KUMA: Tana kasa tana dabo: Kotu ta takawa APC burki a kan zaben Shehu Sani

Don haka sun yi kira ga Oshiomhole da ya chaja shawara ko kuma yayi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar cikin sa’o’i 24 masu zuwa, inda suka sha alwashin zasu dauki duk matakin da ya dace kafin su dangana da kotu don gyara rashin adalcin da shugaban APC yayi masu.

A baya mun ji cewa kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta soke zaben fidda gwani na gwamna a jihar Zamfara.

Kwamitin ta dauki wannan mataki ne bayan ta amince da shawararar kwamitin APC karkashin jagorancin Farfesa Abubakar da aka tura domin su gudanar da zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel