APC ta soke zaben fidda gwani na gwamna a Zamfara

APC ta soke zaben fidda gwani na gwamna a Zamfara

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta soke zaben fidda gwani na gwamna a jihar Zamfara.

Kwamitin ta dauki wannan mataki ne bayan ta amince da shawararar kwamitin APC karkashin jagorancin Farfesa Abubakar da aka tura domin su gudanar da zaben.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke das a hannun mukaddashin sakataren labaran jam’iyyar, Yakini Nabena a Abuja a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba.

APC ta soke zaben fidda gwani na gwamna a Zamfara

APC ta soke zaben fidda gwani na gwamna a Zamfara

A baya mun ji cewa rikicin cikin gida daya dabaibaye jam’iyyar APC reshen jahar Zamfara yazo karshe bayan an sanya ranakun gudanar da zaben fitar da gwanin da zai tsaya mata takarar gwamna har sau uku, amma kuma ana dagewa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa sanya ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben, ba kamar yadda gwamnan jahar yace an dage zaben ba har sai baba ta ji.

KU KARANTA KUMA: FCTA ta dauki nauyin karatun yarinyar da jirgin soji ya buga

Shugaban kwamitin shirya zaben, Dakta Abubakar Fari ne ya tabbatar da wannan cigaban, inda yace matsalar dake tsakanin bangaren gwamnan jahar Abdul Aziz Yari da bangaren yan adawar gwamnan da suka kunshi gagga gaggan yan siyasa kuma yan takara su takwas a yanzu ta kau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel