FCTA ta dauki nauyin karatun yarinyar da jirgin soji ya buga

FCTA ta dauki nauyin karatun yarinyar da jirgin soji ya buga

- Hukumar FCTA ta dauki nauyin karatun yarinyar da hatsarin jirgin soji ya shafa

- Daraktan hukumar ilimi na babban birnin tarayya, Dr Adamu Noma ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci yarinyar a babban asibitin Maitama

- Yace sukolashif din zai fara aiki da zaran an sallame ta daga asibiti

Hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ta dauki nauyin karatun Miss Elizabeth Elijah wacce jirgin sojin sama da yayi hatsari a lokacin atisayar ranar yancin kai ya buge ta.

Daraktan hukumar ilimi na babban birnin tarayya, Dr Adamu Noma ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci yarinyar a babban asibitin Maitama, Abuja, tare da wasu daraktoci da suka wakilci hukumar a ranar Laraba, 3 ga watan Oktba a Abuja.

FCTA ta dauki nauyin karatun yarinyar da jirgin soji ya buga

FCTA ta dauki nauyin karatun yarinyar da jirgin soji ya buga
Source: Depositphotos

A cewarsa hukumar birnin tarayya ta yanke shawarar daukar nauyin duk wani abu da ya shafi karatun ta, inda yayi bayanin cewa sukolashif din zai dauki nauyin dukkanin makarantar ta.

Ya tabbatar da cewa shirin zai fara aiki da zaran an sallame ta daga asibiti.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya fara kokarin sasanta rigimar Jam’iyyar APC a Jihohin Kaduna da Ondo

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahto cewa yarinyar na samun kulawar da ya dace kuma tana samun sauki sosai sannan za’a sallamo ta ba da jimawa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel