Buhari ya fara kokarin sasanta rigimar Jam’iyyar APC a Jihohin Kaduna da Ondo

Buhari ya fara kokarin sasanta rigimar Jam’iyyar APC a Jihohin Kaduna da Ondo

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa ta kai har Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan sa ya sa baki a rikicin Jam’iyyar APC a wasu Jihohin da rigima ke nema ya barke irin su Jihar Kaduna.

Buhari ya fara kokarin sasanta rigimar Jam’iyyar APC a Jihohin Kaduna da Ondo

Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga cikin rigimar APC
Source: Depositphotos

Idan ba ku manta ba, Shugaban kasa Buhari ya gana da Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna da kuma Sanatan Yankin Jihar Shehu Sani wanda Jam’iyyar APC mai mulki ta ba tikitin takara a sama wanda hakan ya kawo rikici.

Wannan mataki da Uwar Jam’iyyar APC ta dauka ne ya sa wani babban Hadimin Gwamnan na Kaduna watau Uba Sani ya sheka Kotu inda ya nemi a fitar da ‘Dan takarar APC na Sanatan Jihar a zaben 2019 ta hanyar zaben fitar da gwani.

Haka dai ake fama da wannan takaddama a Jihar Ondo inda APC ta ke neman Sanata Ajayi Borrofice ya koma kan kujerar sa babu hamayya. Sai dai Gwamna Rotimi Akeredolu ya rantse sai an gudanar da zaben fitar da gwani a APC.

KU KARANTA: Zaben cikin gida: An yi takara tsakanin uwa da 'da a jam'iyyar APC

Yanzu dai Gwamnonin duk sun gana da Shugaban kasa Buhari a fadar Shugaban kasa. Sai dai ba su yi wa ‘Yan jarida bayanin abin da ya kawo su wajen Shugaban kasar ba bayan sun gama ganawa a bayan labule a Aso Rock a makon nan.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Gwamnonin na Jam’iyyar APC Rotimi Akeredolu da Nasir El-Rufai su na cikin wadanda tun farko ba su so tsohon Shugaban APC John Oyegun ya bar kujerar sa ba har ta kai aka nada Adams Oshimhole.

Shugaban APC na kasa watau Kwamared Adams Oshiomhole ne dai yayi kutun-kutun wajen ba wasu ‘Yan takara tikiti a sama a Jam’iyyar. Hakan ya sa wasu su ka fara zanga-zanga su na kira a tsige sa daga mukamin na sa kafin zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel