Ba zan bari a Kunyata Najeriya ba - Buhari

Ba zan bari a Kunyata Najeriya ba - Buhari

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin cewa ko kusa ba zai taba bari Najeriya ta kunyata ba domin kuwa sai dai bayan ran sa a yayin tsayuwar daka ta ci gaba da tsarkake kasar nan daga gurbatanci.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana cewa shugabancin jam'iyyar sa ta APC ba zai gaza ba wajen ci gaba da yiwa kasar nan ta Najeriya tsarki ta fuskar gurbacewar shugabanci da kuma rashawa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sanadin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, da ya bayar da shaidar hakan yayin ganawarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa dake babban birni na tarayya.

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, nan ba da jimawa ba zai kawo karshen duk wata jita-jita wajen gabatar da majalisar yakin neman zaben shugaban kasa da za ta tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a babban zabe na 2019.

Ba zan bari a Kunyata Najeriya ba - Buhari

Ba zan bari a Kunyata Najeriya ba - Buhari
Source: UGC

Ya ci gaba da cewa, ya na sane da muradi gami dakiraye-kirayen al'ummar Najeriya wajen kafa wannan majalisa ta yakin neman zaben sa da za ta tabbatar da nasarar ci gaba da jagorantar kasar har bayan 2019.

KARANTA KUMA: Sakataren PDP na jihar Kwara ya lashe Tikitin Takara na Kujerar Majalisar Wakilai

Shugaba Buhari ya kuma mika godiyarsa gami da kwarara yabo dangane da yadda al'ummar Najeriya suka fito kwansu da kwarkwata wajen bayyana soyayyar su tsagwaranta a gare su domin ganin ya sake share wurin zama a fadar Villa.

Legit.ng ta fahimci cewa, a karshen wannan mako za a gudanar da gangami na jam'iyyar APC a babban birnin kasar nan na tarayya, inda bayan gudanar wannan babban taro za a kafa majalisar yakin neman zaben shugaban kasa kamar yadda jagoran kasar nan ya bayyana.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel