Yan APC a majalisa sun bayyana matakin da zasu dauka akan Dogara da zarar ya bude majalisa

Yan APC a majalisa sun bayyana matakin da zasu dauka akan Dogara da zarar ya bude majalisa

Yayan jam’iyyar APC a majalisar wakilai sun dauki alwashin ganin bayan Kaakakin majalisar a siyasance, Yakubu Dogara ta hanyar tsigeshi daga mukaminnasa ko yaki ko yaso, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dan majalisa mai wakiltar Akoko-Edo na jahar Edo, Peterson Akpata ne ya sanar da haka a ranar Laraba 3 ga watan Oktoba a yayin ganawarsa da yan jaridu a garin Bini, inda yace yayan jam’iyyar APC sun shirya tsaf don aiwatar da umarnin jam’iyyar tasu akan Dogara.

KU KARANTA: Rikici ya barke a jahar Zamfara saboda zaben fidda gwanin takarar gwamna

Peter yace da zarar an dawo zaman majalisa, zasu taru su tsige Dogara daga mukamin Kaakaki tunda dai ya fice daga jam’iyyar APC, wanda itace jam’iyya mai rinjaye a majalisar. “Ba zamu bari dan wani jam’iyya daban ya shugabanci majalisar ba, a matsayinmu na masu biyayya ga jam’iyya zamu yi nazari game da halin da ake ciki.

“Kuma duk matakin daya kama zamu dauka, ba zamu taba jin dadi ba ace dan wata jam’iyyar da bata da rinjaye ya shugabancemu a majalisa ba, wannan haramun ne kada’an, kuma zamu dauki akansa a yadda yake.” Inji shi.

Da yake karin haske akan zabukan fitar da yan takarar jam’iyyar APC na mukamai daban daban kuwa, Peter yace yana muradin komawa majalisa karo na uku, kuma jama’ansa sun amince masa suna goyon bayansa.

Sai dai ya koka kan yadda yan takara ke kashe kudi, don haka yace a duk lokacin da aka zabe fitar da gwani, yan takara na asarar kudade ne, domin kuwa duk kudin da ka raba ma jama’a ba zai dawo ba, sai ma dai ka kara musu kafin sabuwar ranar da aka sanya.

A wani labarin kuma, Kaakakin majalisa Yakubu Dogara ya lashe zaben fidda gwani na takarar kujerar majalisa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP sakamakon babu wani abokin hamayya da yayi kokarin ja da shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel