Jam’iyyar APC ta fatattaki wani Sanata, ta bukaci hukumar DSS da Yansanda suka kama shi

Jam’iyyar APC ta fatattaki wani Sanata, ta bukaci hukumar DSS da Yansanda suka kama shi

Uwar jam’iyyar APC reshen jahar Delta a karkashin jagorancin Cyril Abeye Ogodo ta fatattaki dan majalisa mai wakiltar al’ummar Delta ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, inji rahoton jaridar Sahara reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugabancin Ogodo ta yanke wannan shawarar ne bayan wani taron gaggawa da ta shirya a garin Asaba a ranar Laraba 3 ga watan Oktoba, a inda jam’iyyar ta yanke shawarar sallamar Omo-Agege.

KU KARANTA: Al’ummar garin da aka gano motar Janar Alkali sun fara yin gudun hijira don gudun hukuncin Soja

Jam’iyyar ta zargi Sanatan da yi mata bita da kulli kamar yadda ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar daya samu sa hannun mai baiwa jam’iyyar shawara akan harkar dok, Dennis Nwanokai tana cewa sallamar da aka yi Sanatan ta fara ne nan take.

Jam’iyyar APC ta fatattaki wani Sanata, ta bukaci hukumar DSS da Yansanda suka kama shi

Sanata Omo-Agege
Source: Depositphotos

“Sanata Ovie ya dade yana cin dunduniyar jam’iyyar APC a jahar Delta, na baya bayannan shine daya kwashe kayan zabe da uwar jam’iyya ta kasa ta aiko dasu don gudanar da zaben fidda gwani, inda yayi amfani dasu wajen shirya haramtaccen zaben fidda gwani.

“Sauran laifukan da Sanatan ya tafka sun hada da sauyan sunayen wakilan da zasu zabo yan takarkaru, da kuma yin amfani da yan daba wajen cin mutuncin halastattun wakilan jam’iyya, ya aikata wadannan laifukan ne tare da hadin bakin wasu yayan jam’iyyar da muka dade da kora.

“Don haka jam’iyya na sanar da sallamarshi na dindindin kuma muna kira ga hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, da rundunar Yansandan jahar Delta da su gaggauta kamashi tare da Jones Erue domin su gurfanar dasu gaban kotu saboda suna ma APC sojan gona.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel