Kaico! A zuwa daya mahara yan bindiga sun kashe mutane 14 a jahar Filato

Kaico! A zuwa daya mahara yan bindiga sun kashe mutane 14 a jahar Filato

Akalla mutane goma sha hudu ne suka rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar wata sabuwar rikici data barke a kauyen Jol dake cikin karamar hukumar Riyom a lokcin da yan bindiga suka kai wani mummunar farmaki, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban riko na karamar hukumar Riyom Emmanuel Jugu ne ya tabbatar da kai harin a ranar Laraba, inda yace a daren Talata 2 ga watan Oktoba ne yan bindigan suka kai farmakin a kauyen Jol.

KU KARANTA: Al’ummar garin da aka gano motar Janar Alkali sun fara yin gudun hijira don gudun hukuncin Soja

“Da gaske ne an kai wannan hari, yan bindigan sun kashe mutane goma sha hudu daga ciki akwai mata da kananan yara, hakazalika jami’an tsaron da suka kai dauki sun ga gawarwakin mutane da dama.” Inji Jugu.

Wannan harin ya faru ne bayan kimanin kwanaki biyu da shugaban kasa ya baiwa jama’an jahar Filato hakuri game da hare haren da ake kaiwa tare da yin tir da hakan, inda yayi alkawarin shawo kan matsalar kamar yadda ya fada a jawabinsa na bikin zagayowar ranar samun yancin Najeriya.

Haka zalika shima gwamnan jahar, Simon Bako Lalong ya yi Allah wadai da hare haren, sa’annan yayi kira ga al’ummar jahar dasu zauna lafiya da junansu cikin aminci, kauna da taimakon juna.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin rundunar yansandan jahar, Terna Tyopev yaci tura, haka nan ma kaakakin rundunar hadaka ta Sojoji dake tabbatar da tsaro a jahar, Adam Umar bai amsa kiran da tayi masa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel