Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade biyu

Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade biyu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta mukamin babban likitan dake shugabancin asibitin koyarwa na jami'ar Obafemi Awolowo dake garin Ile-Ife a jihar Osun

- Kazalika shugaba Buhari ya nada Bassey Abasi a matsayin shugaban asibitin koyarwa na jami'ar Uyo, a jihar Akwa Ibom

- Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne ya saka hannu a kan wasikun aikin mutanen da Buhari ya nada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta mukamin babban likitan dake shugabancin asibitin koyarwa na jami'ar Obafemi Awolowo dake garin Ile-Ife a jihar Osun.

Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana wannan shine zango na biyu kuma na karshe da shugaban asibitin, Farfesa Victor Adetiloye, zai yi bayan ya cinye zangonsa na farko.

Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade biyu

Shugaba Buhari
Source: Facebook

Kazalika shugaba Buhari ya nada Bassey Abasi a matsayin shugaban asibitin koyarwa na jami'ar Uyo, a jihar Akwa Ibom. Abasi zai shafe tsawon shekaru 4 yana shugabantar asibitin.

DUBA WANNAN: 2019: Gwamna dake takarar gwamna a PDP ya koma APC

Boade Akinola, darektan yada labarai na ma'aikatar lafiya, ya bayyana cewar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne ya saka hannu kan wasikun aikin mutanen da Buhari ya nada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel