Sakataren PDP na jihar Kwara ya lashe Tikitin Takara na Kujerar Majalisar Wakilai

Sakataren PDP na jihar Kwara ya lashe Tikitin Takara na Kujerar Majalisar Wakilai

Mun samu cewa Sakataren jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara, Razaq Lawal, ya samu nasarar lashe tikitin takara na kujerar Majalisar wakilai na kananan hukumomin Ilorin ta Yamma da kuma Asa yayin zaben fidda gwani da aka gudanar.

A ranar Talatar da ta gabata ne wakilan zaben fidda gwani na jam'iyyar suka tabbatar da nasarar Mista Razaq a babban ofishin ta dake mazabar sa cikin birnin jihar na Ilorin.

Kazalika, tsohon dan majalisa da ya wakilci kananan hukumomin Ilorin ta Gabas da ta Kudu a majalisar wakilai, Honarabul Abdulwahab Issa, ya sake lashe tikitin takarar jam'iyyar PDP na kujerar da ya rika a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

Nasarar Razaq Lawal a matsayin dan takara na jam'iyyar, wani cikar buri ne ga shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, da ya kudurci bai wa dukkanin mambobin jam'iyyar dama walau sababbin shiga ko wadanda suka dade a cikin ta.

Sakataren PDP na jihar Kwara ya lashe Tikitin Takara na Kujerar Majalisar Wakilai

Sakataren PDP na jihar Kwara ya lashe Tikitin Takara na Kujerar Majalisar Wakilai
Source: Depositphotos

Wani Shugaba na jam'iyyar reshen jihar Kwara, Alhaji Adesina Jimoh, ya kwararawa Saraki yabo dangane da wannan sauyin yanayin siyasa da ya kawo cikin jihar da kuma jam'iyyar domin tabbatar da adalci a tsakanin mambobin ta.

KARANTA KUMA: An cafke wani Mutum da laifin lakadawa Agolansa duka har Lahira a jihar Edo

A yayin ci gaba da malalawa Saraki yabo, Alhaji Jimoh ya bayyana cewa shugabanci Saraki na musamman da ba bu kamar sa ya sanya jam'iyyar PDP bisa turba ta cin moriyar hadin kai tare da kara karfin gwiwar cin nasara kan sauran jam'iyyun adawa.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta juya baya ga Sanatan Kano ta Tsakiya, Rabi'u Kwankwaso, dangane da zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar a jihar Kano.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel